Dole ne dalibi ya mallaki Imel kafin yin rajistar JAMB daga ranar 31 ga Janairu

0
193

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta sanar da cewa daga ranar 31 ga watan Junairu, 2023, babu wani dan dalibi da za a yi masa rajista ba tare da an ba shi adireshin Imel ba.

Har ila yau, an shawarci ‘yan dalibai  da su sami ainihin adiresoshin imel kafin su ci gaba da yin rajistar UTME

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Dakta Fabian Benjamin ya fitar jiya, hukumar ta bullo da matakin ne domin tabbatar da cewa an bi ka’idojin da suka dace wajen samun duk wasu bayanai da suka dace.

Sanarwar ta ce: “Hukumar ta lura cewa wannan bitar shawarwarin da ta yi kan rajistar UTME da ke ci gaba da yi shi ne don tabbatar da cewa an bi ingantattun hanyoyin da za a bi wajen samun duk bayanan da suka shafi ‘yan daliban.

“Hukumar ta kara da cewa saban tsarin baya ga taimakawa wajen fitar da bayanai masu dacewa da na zamani na dalibai, haka nan yana da matukar muhimmanci wajen saukaka isar da sakon gaggawa da mahimmanci ga dalibai cikin sauki da inganci.

“Bugu da ƙari, imel ɗin yana ba da ƙarin sassauci a cikin sadarwa kuma hanya ce ta ƙwararru ta isar da dalibai sakonni akan abinda ya shafi jarrabawar.

“Saboda haka, an shawarci daliban da su sami sahihan adiresoshin imel kafin su ci gaba da rajistar UTME.”

Bugu da kari, ya ce daliban su tabbatar da cewa an adana lambobin sirrinsu a tsare saboda hukumar ba za ta dawo wa dalibi lambobin sirrinsa ba  ta imel ba ko canza adireshin imel da zarar an yi rajista.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here