Son rai da rashin cancantar jarumai ke gurbata al’adu a fina-finan mu – Daushe

0
97

Fitaccen Jarumin da ya shahara ya kuma dade a fannin fina-finan barkwanci da ya shafe shekara 28 cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood. RABI’U IBRAHIM wanda aka fi sani da DAUSHE, ya tattauna da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA, inda ya bayyana wa masu karatu matsaloli da kalubalen da ya fuskanta a masana’antar, tare da yin kira ga gwamnati a kan abubuwan da suka kamata a yi domin ci gaban masana’antar Kannywood, har ma da wasu batutuwan da suka shafi rayuwarsa. Ga dai yadda tattaunawar ta gudana:

Da farko za ka fadawa masu karatu cikakken sunanka tare da sunan da aka fi saninka da shi…

Sunana Rabi’u Ibrahim (Daushe).

Ko za ka fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinka?

To Ni dai Rabiu ibrahim (Daushe), an haife ni a karamar hukumar Ajingi cikin Jihar kano, shekara ta 1979 watan Yuni. Na yi makarantar firamare a nan garin Ajingi, wanda daga baya mahaifina ya sami canjin aikin zuwa garin Wudil, cikin Jihar Kano. Nan na ci gaba da firamare da kuma Sakandare, wato makarantar horan malamai ta garin Wudil  ‘T.C Collage Wudil’. Inda na shiga harkokin kasuwanci daga baya.

Ta yaya ka samo sunan Daushe?

Na samo sunan daushe ne a wani gari da ake kira da misau cikin Jihar Bauchi a lokacin da nake koyan Dirama, muna yawo ne da wasu mutane kafin mu hadu da Alh. Rabilu Musa (Dan ibro) a wannan tafiyar da muka yi tafiya ce ta kwatar kai ba ni da sunan da nake amfani da shi a wasa ko a dirama saboda haka sai Jagoran tafiyar ya ce kowa sai ya samo sunan da za a rinka kiransa da shi a fagen dirama, ta nan ne na kirkiro wa kaina suna da Daushe, kin ji ta inda na samo wa kaina sunan Daushe.

Me ya ja hankalinka har ka tsunduma harkar fim?

Ganin kullum hausawa na watsi da Al’adarsu  suna aro wadda ba tasu ba, da kuma sanbada gudummawa wajan tallata kalmar malan bahaushe da tuna masa Al’adunsa da Abincinsa da kuma sake jawo shi nuna masa harshensa na da tasiri a duniya baki daya.

Wacce irin rawa kake takawa a masana’antar Kannywood?

Ina taka rawa mafi mataki na daya shi ne; matsayin uba ko magidanci, ko maigari, ko Alkali, ko sarki, ko dan sanda ko soja ko likita da dai sauran gurare mafi girma a cikin fina-finan Hausa.

Kamar fannin ba da umarni ko shiryawa ko rubutawa ko makamancin haka fa?

Ina rubutun labari da kaina kuma ina ba da umarni, nan take na sha zuwa aiki a matsayin Jarumi sai mai aikin ya ce ni zan ci gaba da ba da umarni, na yi haka ba sau daya ba, ba sau biyu ba. Kuma ina ‘Producing’ da kaina, na sayar ko kuma na ba da kudi a yi min ba tare da an san nawa ne ba.

Ya kake kallon yadda fim ke gudana a yanzu, musamman da ka yi magana a kan al’ada, da yawan mutane na kallon fim din Hausa ba a yin sa bisa al’ada, sai ma wasu al’adun da ake arowa a ko da yaushe, me za ka ce a kan hakan?

Hakan yana da nasaba da barin Al’adunmu da muka yi a baya, da kuma dimaucewar mutanen cikin masana’antar da suka yi da yin aikin son kai ko son rai na rashin duba cancantar Jarumi ko Jaruma, wajan sanya su a gurbin da ya dace.To sun hada kansu da aiki a yanzu dai sakamakon rikon sakainar kashi da akai wa sabgar.

Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance a wancen lokacin?

Aike na kawai ake yi tsahon shekara 7 ina fama da aike da sayan sigari, da siyo wa mata abinci da yi musu wanki, haka nai ta fama.

Lokacin da ka fara tunanin shiga harkar fim, bayan ka sanar da iyayenka, ko akwai wani kalubale da ka fuskanta daga gare su?

Na fuskanta, amma daga baya na ce kawai su yi min Addu’a idan ba alkairi Allah ya canza min kawai.

Za ka ka yi shekara nawa da fara fim?

Zan yi shekara 28, zuwa da tara.

A wanne fim ka fara fitowa kuma wacce rawa ka taka cikin fim din?

Almajirai, na fito a magidanci wanda Almajiran suke shigowa gidana su dauke min Abinci nake fitowa ina ihu ina cewa Ihu  taliyata ‘yar Gwabnati.

Ko za ka iya tuna yawan adadin fina-finan da ka fito ciki?

Ba zan iya ba wallahi Allah, saboda jiya ba yau ba ce, a kalla za su kai dubu goma.

Ya farkon farawarka ya kasance, musamman yadda kake sabo a lokacin?

Na sha fama da kalubale kamar tsangwama da kyara da hantara da wuni da yunwa da kuma  rashin sakar min fuska a gun wadanda na samu a ciki lokacin da na zo na samu abokan aiki.

Me ya sa ka zabi zama a bangaren Camama dan taka rawa ciki?

Saboda shi ne fim din da sako ya fi tafiya ga dan kallo nan take kuma cikin nishadi za ka kalla duk ai da ‘ya’yanka ba tare da jin kunya ba.

Ya za ka bambanta wa masu karatu bambancin fina-finan baya dana yanzu musamman idan ka cire bangaren ‘yan camama da kuke yi ka hada su waje guda?

Bambanci a bayyane yake ai idan kika dubi sa tufafi za ki ga na da, hatta kayan da samari maza ke sakawa hannun rigar har yawa yake yi, saboda tafiya a kan  tsarin Addini da Al’ada.

Akwai wata murya da kake yi cikin fina-finanka wanda kuma a zahiri gashi dai ba haka muryarka take ba, shin koya maka aka yi lokacin da ka fara fim ko kuwa kai da kanka ka kirkiri abarka dan kara armashin shirin?

Ba wanda ya koya min maida hankali da san na birge mai kallona nai ta sarrafa ta har tazama haka a yau.

Akwai wata riga da kake yawan sakawa a cikin mafi yawan fina-finanka, shin rigarka ce kai ka ware ta dan shirin fim kawai, ko kuwa a bangaren aikinku ne na ‘yan camama ake rabawa kowa rigarsa, ta yadda duk shirin da zai yi sai ya dauko ya saka hade da hula ko kuwa?

Kowa ke siyan kayansa ni nake dinka kayata da hular dan dacewa da salona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here