Jamahuriya Nijar: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 2 a Maradi

0
106

Yan bindiga sun kashe mutane biyu a yankin Inyelwa na yankin Madarunfa a Jihar Maradi da wasu biyu a garin Jibiya na Jihar Katsina.

Tun farko dai ‘yan bindigar sun fara kai hari garin Ingelwa na jihar Maradi, inda suka tafi da dabbobi da suka hadar da shanu da rakuma da sauran kananan dabbobi bayan sun hallaka mutane 2, kafin jami’an tsaro da mutanen gari su yi musu tara-tara lamarin da ya yi sanadin mutuwar dan bindiga daya.

Bayan ‘yan bidigar sun kammala barnar ne kuma suka tsallaka karamar hukumar Jibiya ta Jamhuriyar Nijar, inda nan ma suka kashe mutane biyu, abinda ke zuwa bayan wani barin wuta da jami’an tsaro ke yiwa ‘yan bindigar da suka addabi yankunan jihar katsina dama Zamfara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here