Inganta Ilimi: Gwamnatin jihar Gombe ta dauki karin sabbin malamai 1,000 aiki

0
115

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya dauki aiki malaman makarantun sakandare dubu daya aiki don cike gibin da ake da shi a fannin ilimi.

Idan dai za a iya tunawa, kwanaki gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya amincewa Hukumar Kula da Malamai ta jihar (TSC) da ta dauki sabbin malamai 1,000.

Gwamna ya gabatar da takardun daukar aikin a dakin taro na Banquet da ke gidan Gwamnatin Kihar a ranar Asabar.

Gwamna Yahaya, ya bayyana ilimi a matsayin ginshikin duk wani ci gaba, duba da cewa duk wata al’uma da ke son ci gaba da zaman lafiya dole ne ta tabbatar da inganci da samar da ilimi a dukkan matakai.

Yahaya ya bayyana cewa gabatar da takardun daukar aikin ga sabbin malamai 1,000 da kuma wasu 288 da aka sauyawa wurin daga hukumomin kula da ilimi na kananan hukumomi zuwa ma’aikatar ilimi ta jiha, ya biyo bayan wani gagarumin aiki da Hukumar Kula da Malamai ta TSC ta gudanar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here