Fitacciyar yar TikTok Murja ta shiga komar yan sanda

0
148

Ƴan sanda sun kama fitacciyar jarumar wasan barkwanci a TikTok, Murja Kunya a otal din Tahir da ke Kano.

Ƴan sandan sun kama ta ne a lokacin da ta ke kokarin kama wa baƙin ta na kusa da na nesa da za su zo bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta da aka yi ta yadawa.

Ko a watan Satumban shekarar da ta gabata, wata kotun shari’ar Musulunci ta rubuta wa kwamishinan ƴyansandan jihar Kano wasika da ya kama da bincikar Kunya tare da wasu ƴan TikTok bisa zargin lalata tarbiyyar matasa.

Sauran ƴan TikTok da ke cikin wasikar sun hada da Mr 442, Safara’u, Dan Maraya, Amude Booth, Kawu Dan Sarki, Ado Gwanja, Ummi Shakira, Samha Inuwa da Babiana.

A watan Nuwamban shekarar da ta gabata ma, wata kotun majistare ta jihar Kano ta yanke wa wasu matasa biyu Mubarak Isa da Nazifi Bala hukuncin bulala 20, da kuma aikin gwale-gwale na tsawon kwanaki 30 bisa samun su da laifin yin wasan barkwanci na TikTok kan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje.

An yanke wa wadanda ake tuhumar hukuncin ne bisa tuhume-tuhume biyu da suka shafi ɓata suna da kuma tada hankalin jama’a.

MGabari ya kuma umurci wadanda aka yanke wa hukuncin da su biya tarar Naira 20,000 kowannensu, su kuma yi bidiyo ta bada hakuri ga Gwamna Ganduje a shafukan sada zumunta nasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here