Benzema ya karya tarihin Raul Gonzalez

0
99

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Karim Benzema ya zura kwallo a raga a ranar Lahadi bayan kungiyar tasa ta je ta doke Athletic Bilbao 2-0 a wasan mako na 18 a gasar La Liga.

Karim Benzema ne ya fara cin kwallo a minti na 24 da fara kwallo, sannan Toni Kroos ya kara na biyu dab da za’a tashi daga fafatawar kuma kwallon da Benzema ya ci a filin wasa na San Mames ya sa ya yi kan-kan-kan da Raul Gonzalez, a tarihin yawan ci wa Real Madrid kwallaye a raga a La Liga.

Dan wasan dan kasar Faransa ya ci kwallon da yanzu yana da iri daya da ta Raul mai 228, wanda ya yi kwazon nan tsakanin shekarar 1994 zuwa 2010, shi ne na biyu a kungiyar.

Wanda yake na daya a yawan ci wa Real Madrid kwallaye a La Liga shi ne Cristiano Ronaldo mai kwallaye 312 a raga kuma Benzema, wanda yake da kwallo tara a babbar gasar kwallon ta Sifaniya a bana, ya fara ci wa Real Madrid kwallo a tariihi a karawar mako na uku a kakar 2009 zuwa 2010 a fafatawa da Derez.

Kungiyar da Benzema ya ci kwallaye da yawa a La Liga ita ce Getafe da ya zura mata 17, sai Granada da ya ci 14 kuma kyaftin din Real Madrid, shi ne kan gaba a zura kwallaye a La Liga a bara da kwallaye 27, inda kungiyar ta lashe La Liga na 35 jumulla.

Benzema mai rike da kyautar gwarzon duniya ta Ballon d’Or shi ne na biyu a yawan ci wa Real Madrid kwallaye a tarihi, mai 335 kawo yanzu a dukkan fafatawa sannan cikin  kofuna 23 da ya dauka a Real Madrid sun hada da Champions League biyar da Club World Cup hudu da Uefa Super Cup hudu da La Liga hudu da Copa del Rey biyu da Spanish Super Cup hudu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here