Dage ranar wa’adin tsohon kudi ba me yuwa bane – Emiefele

0
133
Godwin-Emefiele
Godwin-Emefiele

Gwamman Babban Bankin Najeriya Godwin Emefeile ya sake jaddada cewa babu gudu babu ja da baya game da wa’adin da babban bankin ƙasar ya saka na daina amfani da tsoffin takardun kuɗin ƙasar.

A wani sakon bidiyo da babban bankin ya wallafa a shaifin sa na Tuwita da maraicen ranar Asabar mista mista Emefiele ya ce ya samu rahotonni kiraye-kirayen da jama’a ke yi na buƙatar ƙara wa’adin da bankin ya saka na daina amfani da tsoffin takardun kuɗin ƙasar.

Saboda wasu dalilai da suka hadar da rashin samun wadatattun sabbin takardun kuɗin, ko ƙurewar lokaci wajen kai tsoffin takardun kuɗin zuwa bankuna.

Mista Emefiela ya ce ”hakika ina ɗauke da sako maras daɗi ga waɗanda suke tunanin za mu ƙara wa’adin, dan haka ina mai bayar da haƙuri a kan haka, domin kuwa ba abu ne mai yiyuwa b”.

”Dalili kuwa shi ne kamar yadda shugaban ƙasa a faɗa har sau biyu cewa kwanaki 100 sun isa duk wanda yake da tsoffin kuɗi da ya je ya musanya su a bankuna”, in ji Emefeile

Ya ƙara da cewa ”mun ɗauki duka matakan da suka dace domin tabbatar da cewa bankuna sun kasance a buɗe domin karɓar tsoffin takardun kuɗi, kuma mun yi imanin cewa kwana 100 sun wadatar a yi hakan”.

Ya ce bankunan ƙasar za su ci gaba da kasancewa a buɗe a ranakun asabar da Lahadi domin sauƙaƙa wa jama’a wahalhalun da suke sha.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here