Ronaldo ya gaza a gasar Super Cup ta Saudiya

0
107

Cristiano Ronaldo ya sha kaye na farko na gasa a Saudiya, tun bayan sauyin shekarsa zuwa kungiyar Al Nassr daga Manchester United.

Al Nassr wadda Ronaldon ya yi wa kaftin, ta sha kashi ne a wasan da ta kara da Al Ittihad da kwallaye 3-1 a gasar Saudi Super Cup a daren jiya Alhamis, abinda ya sa suka fice daga gasar. 

A wasan farko da Ronaldo ya buga a gasar kwallon kafar Saudiya Al Nassr ta samu nasarar doke kungiyar Ettifaq da 1-0. 

Tun bayan wasan sada zumuncin da suka buga da PSG inda ya ci kwallaye 2, har yanzu Ronaldo bai samu nasarar ci wa Al Nassr kwallo a wasa na cikin gasa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here