Dalilin da ya sa Google take cewa Aliko Dangote ne mamallakin Najeriya idan an tambayeta

0
130

Akwai maganganu da dama da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke nuna cewa hamshakin attajirin nan, Aliko Dangote, shi ke da ‘Mallakin Nijeriya’, sakamakon yadda manhajar yanar gizo ta Google ke bayyana wa duk sadda aka tambayeta ‘waye mamallakin Nijeriya?’.

Hakan yana nuna cewa, a ‘yan lokutan nan shafin bincike na manhajar Google yana ci gaba da habaka bayanan da ba daidai ba ko kuma in baida bayanan da ya dace, sai ya zukulo abu na kusa daga rumbun tattara bayanai na Wikipedia.

Har ila yau, a ranar Alhamis, wasu masu amfani da shafukan sada zumunta na Nijeriya sun tambayi Google “Waye mamallakin Nijeriya” manhajar binciken ta Google sai ta bayyana bayanan Aliko Dangote daga Wikipedia a sakamakon haka, wanda ya sa bayanan karya da farfaganda suka yadu a twitter.

LEADERSHIP ta gudanar da binciken a Google don tabbatar da amsar tambayar, sakamakon binciken ya nuna Aliko Dangote.

 

Sai dai kuma an gudanar da irin wannan binciken a wasu kasashe kuma sakamakon ya nuna babban attajirin kowace kasa ake sanya wa a matsayin wanda ya mallaki wannan kasa. Haka ma lamarin ya kasance ga kasar Sin, inda aka nuna Jack Ma a matsayin mamallakin kasar Sin.

 

Wannan kuskure ne kawai daga manhajar bincike ta Google.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here