Zulum ya karbi ‘yan gudun hijira 1,300 daga hannun Kamaru

0
91

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya karbi kashi na biyu na karin ‘yan gudun hijirar Nijeriya 855 da aka dawo da su gida daga kasar Kamaru.

Jami’an kasar Kamaru karkashin jagorancin gwamnan yankin Arewa, Minjinyawa Bakari ne suka mika ‘yan gudun hijirar ga Zulum a wani taron bankwana da aka yi a yankin Maroua ranar Talata.

Bakari, a lokacin da yake gabatar da kayan abinci ga ‘yan gudun hijirar, ya sanar da rufe sansanin‘yan gudun hijirar da yawansu ya kai 1,300.

Zulum, a madadin Nijeriya, ya godewa shugaban kasar Kamaru, da sauran jami’ai da wajen dawo da ‘yan gudun hijirar bayan shafe kusan shekara tara a Kamaru.

Gwamnan ya yaba da gudunmawar da shugaba Biya ya bai wa ‘yan gudun hijirar.

‘Yan gudun hijirar Nijeriya 855 da ke zaune a sansanin Minawao sun samu tarba daga al’ummar da ke kan iyakar Nijeriya da Kamaru, kusa da Banki a karamar hukumar Bama ta shugaban kwamitin rikon kwarya, Hon Grema Terab.

Kowane daga cikin ‘yan gudun hijirar ya karbi Naira 40,000 daga Gwamnatin Tarayya da buhun shinkafa, buhun wake, man girki da kudi Naira 60,000.

Ofishin Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) a Kamaru karkashin jagorancin Madam Kimberly, ta ziyarci sansanin Banki, inda ta yaba da kokarin da gwamnatin Zulum ke yi na inganta rayuwarsu.

“Abin ban sha’awa ne sosai tare da hangen nesa da ake bukata don kawo karshen matsalolin ‘yan gudun hijira,” in ji ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here