Na’ura za ta fara tona asirin direbobi masu shan giya a Najeriya

0
84

Ya zuwa karshen shekarar da ta gabata, Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO, ta kiyasta adadin mutane kusan dubu 50 suka rasa rayukansu a Najeriya a sanadiyyar haddura akan hanyoyin kasar, yayin da Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasar ta bullo da wani sabon shiri na amfani da wata na’ura da za a rika yi wa direbobi gwaji da ita don sanin ko sun sha barasa ko kuma a’a.

Wannan adadi, ya wakilci kusan kashi 3 na daukacin alkaluman wadanda suka mutu ta wannan hanya a fadin duniya, kana Najeriya ce ta zamo ta 54 a yawan haddura a kan hanyoyi a duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here