Gwamnatin Najeriya ta musanta kara farashin man fetur

0
115

Gwamnatin Najeriya ta ce koda sunan wasa ba ta amince da wani shirin kara farashin man fetur ba, kuma ba ta bada umurni ga wani ko wasu kungiyoyi su kara ba, a daidai lokacin da jama’ar kasar ke fama da karancinsa.

Karamin ministan man fetur Timipriye Sylva ya sanar da haka bayan rahotanni da dama sun ce gwamnatin ta amince da karin farashin man da take sayarwa dillalai zuwa naira 185.

Sylva ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari bai amince da shirin kara farashin man fetur ko kuma wani nau’i na man da suka hada da dizil ko kuma kananzir ba.

Ministan ya ce babu wani dalili da shugaba Buhari zai sauya alkawarin da ya yiwa ‘yan Najeriya na adawa da kara farashin man a wannan lokaci, domin kuwa ya na sane da irin matsalolin da jama’a suke fuskanta, yayin da ya sha alwashin cewar ba zai dauki wani karin matakin da zai wahalar da su ba.

Sylva ya zargi sanar da karin farashin man a matsayin wani yunkuri na batawa gwamnatin kasar suna da kuma irin sake fasalin tafiyar da bangaren man da hukumomi suka yi.

Ministan ya roki ‘yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu, yayin da gwamnati ke kokarin kawo karshen wannan matsala ta wahalar da talakawa su ke sha wajen samun man.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here