Faransawa za su yi gagarumin yajin aiki a gobe

0
139

Jiragen kasa sun daina aiki, an  kuma rufe makarantu a yayin da  ake shirin shiga wani gagarumi yajin aiki a Faransa a wannan Alhamis, don nuna adawa da shirin shugaba Emmanuel Macron na sake fasalin dokar fanshon kasar a kokarin da yake yi na kara wa kansa maki a siyasance a kasar da ke fama da matsaloli

Shirin shugaba Macron na dage shekarun da ya kamata ma’aikaci ya ajiye aiki daga 62 zuwa 64, yana fuskantar turjiya daga gamayyar kungiyoyin kwadago, sannan bai samu tagomashi a bangaren ra’ayoyin jama’a ba.

A siyasance, lamarin ya yi tsauri ga gwamnatin da ba ta da gagarumin rinjaye a majalisar dokokin kasar, inda a halin da ake ciki masu sassaucin ra’ayi da masu tsananin tsatsauran ra’ayi suka shafa wa idanunsu toka, suna fatali da kudirin shugaban kasar.

‘Yan sanda da jandarmomi sama da dubu 10 ne,  ciki har da dubu 3 da 500 a birnin Paris kawai, za a tura don  sanya ido a kan masu zanga-zangar a cewar Ma’aikatar Cikin Gidan kasar, wadda ke ganin akwai masu zanga-zanga a Paris da ka iya bigewa da tsageranci.

Mahukuntan Faransa sun yi  kira ka da a mayar da zanga-zangar lamari na dakile harkokin tafiyar da kasar, tare da bayyana fatan cewa, ba za ta yi  karko ba, ganin cewa ana iya shiga halin kunci a kasar.

Yanzu haka dai Kungiyar  Ma’aikatan Sufurin Jiragen sama da na jiragen kasa sun kasa sun tsare, don ganin cewa al’amura ba su tafi yadda mahukunta ke so ba a bangarorinsu.