‘Yan Najeriya miliyan 25 na cikin barazanar yunwa a 2023

0
149

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, kusan ‘yan Najeriya miliyan 25 za su fuskanci bala’in yunwa tsakanin watannin Yuni zuwa Agustan wannan shekara ta 2023, muddin ba a dauki matakin gaggawa ba.

Adadin dai kari ne kan mutane miliyan 17 da ke cikin hadarin gamuwa da yunwar a Najeriya wanda aka yi hasashe tun a can baya.

Sanarwar da Hukumar Bunkasa Ilimin Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a shafinta, ta ce, rikice-rikice da matsalar sauyin yanayi da tashin farashin kayayyakin abinci, su ne ummul-haba’isin jefa ‘yan Najeriyar cikin kangi yunwa.

Sanarwar ta ce, an gaza samar da abinci a jihohin Borno da Adamawa da Yobe da ke yankin arewa maso gabashin Najeiya sakamakon tashe-tashen hankula, ga kuma hare-haren ‘yan bindiga a jihohin Katsina da Sokoto da Kaduna da Benue da kuma Niger.

Alkaluman da Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Najeriya NEMA ta fitar sun nuna cewa, matsalar ambaliyar ruwa da aka gani a bara, ta lalata sama da kadada dubu 676  na gonaki, lamarin da ya sa aka samu karancin girbi tare da fuskantar barazanar karancin abinci a kasar.

Bayanai na nuni da cewa, ambaliyar ruwan dai, na daga cikin tasirin sauyin yanayi da ke addabar duniya.