NDLEA ta kwace kwayar Naira biliyan 5 a Lagos

0
105

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta tarwatsa wani gungun masu safarar kwayar Tramadol a birnin Lagos, inda ta kwace miliyoyin kwayoyin da kudinsu ya zarta Naira biliyan 5 a karshen  makon nan.

Darekta a Hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi a birnin Abuja, inda ya ce, jami’ansu sun yi nasarar kwace kwayoyin ne a unguwar Amuwo Odofin da ke jihar Lagos  bayan sun fara cafke biyu daga cikin shugabannin masu safarar.

Jami’in ya kara da cewa, NDLEA ta yi amfani da na’ura wajen gano maboyar wadannan miyagu a unguwar ta Amuwo Odofin, inda suka tara tulin kwayoyin na tramadol a wani katafaren gidan ajiyar kayayyaki.

Daga cikin abubuwan da NDLEA ta kwakwulo daga wannan gida, har da kwayoyi har guda miliyan uku da dubu 264 da 630 na tramadol.

Ga kuma kwalaben hodar iblis har guda dubu 3 da 490, sai kuma kwayar Pregabalin har guda dubu 915.

Tuni shugaban hukumar ta NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, ya yi jinjina ta musamman ga jami’ansa da suka yi bajintar tarwartsa wannan gungun ‘yan kwayar a birnin Lagos.