Gwamnatin Gombe ta nada sabbin shugabannin da za su rike kananan hukumomi

0
137

Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da nada shugabannin riko na kananan hukumomin jihar su goma sha daya 11 domin su jagoranci ragamar tafiyar da harkokin kananan hukumominsu.

LEADERSHIP Hausa dai ta nakalto cewa, wannan matakin dai na zuwa ne bayan karewar wa’adin zababbun shugabannin kananan hukumomin a kwanakin baya wanda tunin aka rushesu.

Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi shi ne ya fitar da sanarwar nadin shugabannin kananan hukumomin a ranar Talata tare da cewa nadin nasu ya fara aiki ne nan take.

Kamar yadda sanarwar ta yi nuni, Abubakar Usman Barambu, shi ne shugaban riko na karamar hukumar Akko; Garba Umar Garus, karamar hukumar Balanga; Margret Bitrus, karamar hukumar Billiri; Jamilu Ahmed Shabewa, karamar hukumar Dukku, yayin da Ibrahim Adamu Cheldu ya zama shugaban riko na karamar hukumar Funakaye.

 

Sauran shugabannin rikon sun hada da Aliyu Usman Haruna, shugaban karamar hukumar Gombe; Faruk Aliyu Umar, karamar hukumar Kaltungo; Ibrahim Buba, karamar hukumar Kwami sannan da kuma Salisu Shu’aibu Dendele a matsayin shugaban riko a karamar hukumar Nafada.

 

Kazalika, Yohanna Nahari da Garba Usman sun zama shugabannin riko na kananan hukumomin Shongom Y/Deba bi da bi.