Ko wa Allah ya bai wa mulkin Kano za mu bi shi – Gawuna

0
144

Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar gwamnan jihar ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki Nasiru Yusuf Gawuna ya ce ko wa Allah ya bai wa mulkin jihar za su bi shi su kuma ba shi shawara, domin ciyar da jihar gaba.

Ɗan takarar ya yi wannan maganar ne a lokacin wata muhawara tsakanin ‘yan takarar gwaman jihar Kano da BBC Hausa ta gabatar ranar Asabar.

Gawuna ya ce ”idan Allah ya so ya ba mu muna addu’ar ya yi riƙo da hannunmu za mu hidimta wa al’umma; idan kuma Allah bai ba mu ba, ko wa Allah ya bai wa za mu bi shi, kuma za mu ba shi shawara ta gaske, domin a samu ci gaban al’ummar jihar Kano”.

Ɗan takarar ya kuma sake nanata kiran al’ummar jihar da cewa a zaɓi cancanta a lokacin zaɓen gwamnan da ke tafe ”a duba mutumin da ya cancanta a zaɓa”.

Ya kuma ce a yi siyasa cikin lumana, domin kuwa ”Mu ‘yan takarar duka da muka zo nan BBC Hausa ta sauke mu a ɗaki ɗaya kuma duka muka gaisa tare da mutunta junanmu”,.

”Dan haka ina kira ga magoya bayanmu da su zauna lafiya’ in ji Gawuna