An kashe masu garkuwa da mutane 3 a arewacin Kamaru

0
125

Akalla masu garkuwa da mutane uku aka kashe a yankin Arewacin Kamaru, a cewar majiyoyin tsaro na cikin gida.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce an kashe masu garkuwa da mutane ne a ranar Lahadin da ta gabata a wani samame da dakarun kasar Kamaru, suka kai a yankin Mayo-Rey.

“Suna dauke da muggan makamai, amma dakaru sun kwace makamansu. An tabka kazamin fada tsakaninsu da dakarun kafin a kashe su,” in ji wani babban jami’in sojan kasar.

Sojojin sun kara kaimi wajen tabbatar da tsaro a yankin da aka ce ana samun yawaitar sace-sacen mutane don neman kudin fansa.

A ranar Litinin ne rundunar Gendarmerie a kasar ta ce dakarunta sun kuma kama wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a yankin Demsa.