Ambaliyar ruwa ya shafi nutane 24,714 a Abuja

0
112

Hukumar Kula da Babban Birnin Tarayya (FCTA), ta ce mutane 24,714 ne ambaliyar ruwa ya shafa a wasu sassan babban birnin kasar nan a shekarar 2022.

A karshen mako ne babban daraktan hukumar bayar da agajin gaggawa ta babban birnin tarayya Abuja, Abbas Idriss, ya bayyana hakan.

Haka kuma, mutane 2,972 ne suka rasa matsugunansu a gundumar AMAC, sannan gidaje 102 sun lalace, yayin da kuma aka ceto rayukan 9,813.

A cewarsa, a karamar hukumar AMAC, mutane 20,376 abum ya shafa, sai kuma 2,058 a karamar hukumar Bwari.

A lokaci guda kuma, a yankin Abaji an samu rahoton ambaliyar ruwa da ta shafi mutum 2,280.

“A karamar hukumar Bwari, ambaliyar ta shafi mutane 2,058 a Dutse Makaranta; a karamar hukumar Abaji, mutane 2,280 ne abun ya shafa a yankin Sarkin Pawa.