2023: INEC ta musanta sake fitar da sunayen ‘yan takara a matakin karshe

0
116

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta musanta wani rahoton da wata kafar yada labarai ta fitar da ke cewa hukumar ta sake fitar da jerin sunayen ‘yan takara na zaben 2023 a matakin karshe.

“Ba wani jerin sunayen ‘yan takara da hukumarmu ta fitar a ranar Lahadi 8 ga watan Janairun 2023 a matsayin jerin sunayen na karshe.”

Wannan matakin na matsayin karyata rahoton da wata jarida da ba (LEADERSHIP ko LEADERSHIP Hausa) ta wallafa ba a ranar Litinin.

Shugaban sashin yada labarai na hukumar, Festus Okoye, shi ne ya shaida hakan ta cikin wata sanarwar da ya raba wa ‘yan jarida a Abuja a ranar Litinin.

Okoye, ya ce, babu yadda za a yi su fitar da sunayen ‘yan takara na karshe a sauran kwanaki 46 da babban zabe.

Ya ci gaba da cewa, babu wani ko wasu sunan ‘yan takara da za su wallafa illa kawai wadanda kotuna suka yi umarni a canza wasu cikin wadanda aka wallafa tun da farko.

Okoye ya yi waiwaye kan jerin sunayen ‘yan takarar na zaben 2023 ya kuma ce tuni sun wallafa su akalla kwanaki 150 kafin ranar zabe domin mutunta dokar zabe ta 2022 da ke sashe na 32(1).