Kaduna: Zan fitar da ku daga talauci – Asake

0
111

Dan takarar gwamna na jam’iyyar Labour Party (LP) a jihar Kaduna, Mista Jonathan Asake, ya ce idan ya yi nasara a zaben watan Fabrairu da Maris, zai fitar da ‘yan kasa daga cikin “ Talauci mai dimbin yawa”.

Ya ce hakan zai maido musu fatan samun ingantacciyar rayuwa mai dorewa.

Asake ya bayyana haka ne ranar Asabar a Kaduna a wani taron tattaunawa na siyasa daya da daya da ‘yan takarar gwamna kan tsarinsu.

Wata kungiyar farar hula (CSO) da Partnership for Issues-Based Campaign in Nigeria (PICaN) da kuma wayar da kan mata kan harkokin shari’a (LAWN) ne suka shirya jerin tattaunawar manufofin, ‘Agenda’.