NFIU za ta haramta fitar da tsabar kudi daga asusun gwamnatocin Najeriya

0
145

Hukumar kula da ke kula da yadda ake hada-hadar kudade a Najeriya, NFIU, ta haramta fitar da tsabar kudade daga dukkan asusun gwamnati, dokar da za ta  fara aiki daga ranar 1 ga Maris da ke tafe.

Daraktan hukumar Modibbo Tukur ne ya sanar da shirin fara aiki da wannna doka yayin taron manema labarai, a Abuja, inda ya yi gargadin cewa duk wanda aka samu da laifin bijirewa zai fuskanci daurin shekaru uku a gidan yari.

Tukur ya ce lura da suka yi da yadda ake samun karuwar fitar da makudan kudade kuma tsabarsu daga asusun gwamnati fiye da kima, ya sanya aka dauki matakin cewa dole daga yanzu a koma amfani da tsarin hada-hadar kudade ta kafar Intanet kamar yadda babban bankin Najeriya CBN ya tanada, domin ta haka ne kawai, za a kiyaye gaskiya da rikon amana akan dukkanin abin da ya shafi kuddaden al’umma.

Jami’in ya kara da cewar duk da dokar cire kudade da ke aiki a Najeriya, gwamnatocin jihohi sun fitar da jimillar tsabar Naira biliyan 701 sama da adadin Naira biliyan 225 da gwamnatin tarayya ta fitar da kuma Naira biliyan 156 da kananan hukumomin kasar nan suka fitar, wanda hakan ya kawo jimillar kudade tsaba da aka fitar asusun ma’aikatun gwamnati tsakanin shekarar 2015 zuwa yau zuwa Naira tiriliyan 1 da biliyan 82.