Wasu ‘yan bindiga sun kona ofishin ‘yan sanda

0
105

Wasu ‘yan bindiga sun kona ofishin ‘yan sanda da ke Ihiala, lamarin da ya haifar da fargaba a kauyuka da sauran al’ummomin yankin.

Wasu gine-ginen da ke tashar sun kone gaba daya kuma ba a tabbatar da dalilinsu na yin hakan ba.

Wani ganau ya ce bayan harin da aka kai ofishin ‘yan sanda da ke kan titin Onitsha zuwa Owerri, sai da masu ababen hawa da ke zuwa Owerri ko kuma daga Owerri suka yi amfani da titin Okija-Uli don wuce Ihiala.

Wani ganau ya ce: “Wasu gungun matasa dauke da makamai sun kai hari ofishin ‘yan sanda na Ihiala a jiya kuma an lalata yawancin gine-ginen. Tun a wancan lokaci ana ci gaba da kai hare-haren adduna a kan mahaya Okada, kuma har yanzu ana jin karar harbe-harbe a yankin.

Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra wadda ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce ana ci gaba da gudanar da aikin a can.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, PPRO, Mista Tochukwu Ikenga ya ce ‘yan bindigar sun jefa bama-bamai a cikin ofishin.

Ya ce: “Da sanyin safiyar yau 28/12/2022 jami’an mu sun yi artabu da wasu ‘yan bindiga da suka kai hari a hedikwatar ‘yan sanda na Ihiala inda suka kwato bindiga kirar Ak47 guda daya da aka yi watsi da su. “’Yan bindigar sun tsere daga wurin ne saboda karfin wuta da jami’an ‘yan sandan suka yi, kuma ba a samu asarar rai ba.

“Abin takaici, bama-baman da ‘yan bindigar suka jefa a cikin ofishin ‘yan sanda tuni suka kunna wuta tare da shafar ginin.