Sharudda 3 da Mbappe ya bai wa PSG idan tana so ya ci gaba da zama

0
193

Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa na PSG Kylian Mbappe ya baiwa kungiyar sharuda uku idan har ba ta son ya bar ta a karshen kakar bana.

A cewar jaridar OK Diario da ake wallafawa a Spain, ta ruwaito cewar Mbappe wanda ya sanya hannu a sabuwar kwantiragi da PSG a farkon wannan kaka, ya ce sharadin farko na ci gaba da zaman sa shine abokin wasan sa Neymar ya bar kungiyar.

Haka nan ya bukaci PSG ta sauya mai horas da su Christophe Galtier da tsohon mai horas da Real Madrid Zinedine Zidane.

Sharadin sa na karshe shine PSG ta kawo dan wasan gaban Tottenham Harry Kane, wanda ake ganin dan wasan na son taka leda da shi.

Idan dai ba’a manta ba a farkon kakar wasan bana, an alakanta dan wasan da komawa kungiyar Real Madrid, sai dai daga bisani dan wasan ya sauya tunani wajen tsawaita kwantiragin sa da PSG har zuwa karshen kaka ta shekarar 2024/2025.

Akwai dai alamu da ke nuna cewar dan wasan baya jin dadin ci gaba da zama a kungiyar ta sa.