Gwamnatin Taliban ta haramtawa mata yin aiki

0
153

Hukumomin Taliban sun umarci kungiyoyi masu zaman kansu da su dakatar da daukar mata aiki saboda rashin bin ka’idojin da suka dace, sanarwar da ke zuwa kwanaki hudu bayan da aka hana ‘yan mata karatu a jami’a saboda irin wadannan dalilai.

Ma’aikatar da ke da alhakin amincewa da lasisin kungiyoyi masu zaman kansu da ke aiki a Afganistan, ta ce ana fuskantar tarin matsaloli da suka hada da korafe-korafe game da rashin saka hijabin musulunci da rashin bin sauran dokoki da ka’idoji da suka shafi aikin mata a kungiyoyin kasa da kasa.

Gwamnatin Taliban ta yi barazanar soke lasisin kungiyoyi da za su kaucewa wadanan umarni ba tare da aiki da wasikar wacce aka aika zuwa ga kungiyoyi masu zaman kansu na kasa da kasa ba.

Wasu kungiyoyi masu zaman kansu guda biyu na kasa da kasa da kamfanin dillancin labaran AFP ya zanta da su, sun tabbatar da cewa sun samu sanarwar ma’aikatar.

Sanarwar ta zo ne kwanaki hudu kacal bayan da gwamnatin Taliban ta yanke shawarar haramta wa matan Afganistan shiga jami’o’in gwamnati da masu zaman kansu a cikin kasar na wani lokaci mai tsawo.

Ministar ilimi mai zurfi, Neda Mohammad Nadeem, ta bayyana kwanaki biyu bayan wannan sanarwar cewa ta dauki wannan matakin ne saboda “daliban da suka je jami’a ba su mutunta umarnin sanya hijabi”.

“Hijabi wajibi ne a Musulunci,” in ji shi, yayin da yake magana kan yadda mata a Afganistan su rufe fuskokinsu da dukkan jikinsu.