Tinubu yayi alkawarin sake fasalin tattalin arzikin Najeriya

0
115

A ranar Alhamis din da ta gabata ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya yi wa ‘yan kasuwa alkawarin cewa idan aka zabe shi zai sake mayar da Nijeriya baya domin samun damammaki da ci gaban ‘yan kasa.

Ya kuma yi alkawarin bayar da himma wajen samar da ingancin harkar tsaro a kasar nan domin baiwa ‘yan kasuwa damar samun muhallin gudanar da kasuwancinsu.

Tinubu ya yi wannan alkawarin ne a wani liyafar cin abincin rana tare da ‘yan kasuwa a Legas.

An gudanar da taron cin abincin rana, mai taken “Gaba da Kasuwanci”, a “Wings” dake kan Tsibirin Victoria.

Dangane da batun tallafin man fetur, ya ce idan aka zabe shi zai dauki kwakkwaran shawarar da za su mayar da tattalin arzikin kasar.

Ya ce: ‘Najeriya ba za ta ci gaba da bayar da tallafin man fetur a kasashe makwabta ba.

Ta yaya za mu iya ba da tallafin man fetur na Kamaru, Nijar, da Jamhuriyar Benin? Ko da yaushe za ku yi zanga-zangar, za mu cire tallafin man fetur.

“Na farko, babban nauyin da ke wuyan gwamnati shi ne ta kare rayuka, dukiyoyi da ci gaban al’ummarta.

Ya ce a matsayinsa na gwamnan jihar Legas, gyara matsalar tsaro a wancan lokacin shi ne abin da ya sa a gaba.