Tarihin rayuwar fitaccen jarumi kuma mawaki a masana’antar Kannywood Ado Isah Gwanja

0
233

Gabatarwa

A wannan karon ma Hausa24 tazo muku da tarihin fitaccen jarumi kuma mawaki a masana’antar Kannywood Ado Isah wanda kukafi sani da (Gwanja) tun daga shekarunsa na kuruciya har izuwa shigar sa masana’antar Kannywood.

Wanene Ado Isah (Gwanja)

Ado Isah Gwanja an haife shi 22 ga Janairu 1990 mawakin Najeriya ne kuma jarumi a masana’antar fina-finan Arewacin Najeriya da aka fi sani da Kannywood. 

Gwanja dai ya fara fitowa a fina-finai ne a shekarar 2017, amma ya dauki tsawon lokaci a harkar waka kafin ya fara wasan kwaikwayo. Gwanja sau da yawa an fi saninsa a waka fiye da a fim, gwanja ya kware a wakokinsa na mata, ana gayyatarsa ​​zuwa bukukuwa inda yake rera wakokinsa, gwanja ya nada tsohon mawakin Hausa Aminu Mai Dawayya a matsayin jagoransa.

Wasu daga cikin fitattun wakokin Gwanja akwai Kujerar Tsakar Gida, Mamar-Mamar, ÆŠakin Ba ciwonwa, Asha Rawa-rawa, Kilu ta Ja Bau, Kidan Mata, Warr da Chass da sauransu.

NBC ta haramta waƙar 'Warr' ta Ado Gwanja a Najeriya - BBC News Hausa

Kundin wakokin sa

Wadannan sune jerin kundayen wakokin sa

 

  • Suna                                         Shekara

  • Kujerar Tsakar Gida.              2014

  • Indonesia                                  2017

  • Matan Arewa                            2016

  • Yuli                                             2018

  • Ga Gwanja                                2017

  • Tangaran                                   2021

  • Adama                                       2021

Kyaututtukan daya samu

Gwanja ya samu kyaututtuka da dama daga daidaikun mutane da kungiyoyi, daga cikin manyan lambobin yabo da Gwanja ya samu akwai kyautar da uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta bayar. Sauran kyaututtukan sun hada da;

  • 2019 ya Samu Gwarzon Jarumin Kano.

  • 2018  ya lashe kyautar Sani Abacha Youth Center ta gwarzon dan wasa.

  • 2018 Kungiyar Dalibai ta kasa (NANS) ta bashi kyautar gwarzon mawakan mata.

  • 2019 kamfanin nishadi na(RS) sun bashi kyutar Mafi kyawun MawaÆ™i na shekara b Ya Lashe.

  • 2018 yayi nasarar zama babban jarumin na (Rhymes Pillars Crew).

MUSIC:ADO GWANJA - WAKA CASS DOWNLOAD MP3

Iyalan sa

Mahaifin Ado Gwanja Bahaushe ne dan Kano kuma mahaifiyarsa ‘yar kabilar Shuwa Arabia ce daga jihar Borno, gwanja musulmi ne, ya yi aure da diya daya.

Karshen tarihin Ado Isah (Gwanja)

Anan ne muka kawo karshe tarihin fitacce jarumi kuma mawaki a masana’antar shirya fina-finan hausa ta Kannywood kenan ku biyomu a Haua24.ng a wani lokacin domin samu cikakkun labarai game da manyan jarumai na masana’antar ta Kannywood harma.