Sheikh Muhammed Niass ya ba Tinubu Babban mukami a darikar Tijjaniya

0
98

Babban Khalifan Darikar Tijjaniya na duniya, Sheikh Muhammad Ibrahim Niass, ya ba Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mukamin Babban Khadi na darikar.

An nada Tinubu wannan mukamin yayin da ya halarci taron Mauludin Duniya da aka gabatar a Nijeriya na Jam’iyyatul Ansarul Deeni Attijjaniya, a filin sukuwar Dawaki da ke Minna, Jihar Neja, ranar Asabar.

Taron Mauludin ya samu halartar gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello; takwaransa na jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje; Etsu da Sarkin Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar.

Sauran Mahalarta taron sun hada da dan takarar gwamnan APC a jihar, Muhammed Umar Bago, da tsohon kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Dimeji Bankole, da sauran manyan baki.