An cafke wani mutum yana wanka da jini a bakin rafi a Ogun

0
106

Wani dan shekara 49 mai suna Ganiyu Shina da ke zaune a garin Abeokuta a Jihar Ogun, ya fada komar ‘yansandan jihar bisa samunsa yana wanka da jini.

Shina an kama shi ne a yayin da yanke kan yin wannan da jinin a bakin rafi dauke wani abu a cikin roba da ake zargin jini ne.

Wasu mazauna yankin Kotopo da ke a karamar hukumar Odeda a jihar, sun ce sun hango Shina yana yin wanka da wani abu da suke zargin jini ne a bakin rafin, inda nan take suka cafke shi.

An ruwaito cewa, Shina ya zo wurin a cikin wata motar haya kirar Nissan, inda ya ajiye ta a gefen hanya ya kuma fito da abun da ake zargin cewa jini ne, ya fara yin wanka da shi.

A lokacin da yake yin wannan, da ya gano ana kallonsa sai ya nemi ya tsere, inda mutane suka yi masa kofar rago, suka cafke shi suka mika shi ga ‘yansanda.

 Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, Shina ya yi ikirarin cewa wani boka ne ya umarce shi da yin hakan saboda matsalolin rayuwar da yake fuskanta.
Oyeyemi ya ce, ya yi ikirarin cewa, jinin da aka same shi da shi, na Saniya ne ba na mutum ba.