Amurka ta gargadi China da Rasha kan nahiyar Afirka

0
102

Amurka ta yi gargadin cewa China da Rasha na tada zaune tsaye a Afirka tare da ci gaba da samun guraben zama a nahiyar, ta hanyar yiwa shugabannin Afirka alkawarin ba da tallafin biliyoyin daloli.

Shugabannin Afirka arba’in da tara ne suka halarci taron koli na farko na nahiyar da Amurka a cikin shekaru takwas, daidai lokacin da shugaba Joe Biden ke neman yin amfani da diflomasiyya don karfafa alaka da yankin.

Sakataren tsaro Lloyd Austin, a wani taro tare da shugabannin kasashen Afirka da dama a farkon taron na kwanaki uku, ya zargi abokan hamayyar Amurka da yin amfani da wata hanya ta daban wajen kulla hulda da kasashen nahiyar.

Austin ya ce, kasar China tana fadada sawun ta a Afirka a kowace rana ta hanyar karuwar tasirin tattalin arzikinta.

Biden na shirin zuba dala biliyan 55 ga Afirka cikin shekaru uku, Fadar White House ta ce Amurka za ta zuba jarin dala biliyan 4 nan da shekarar 2025 don horar da ma’aikatan kiwon lafiya na Afirka.