HOTUNA: Sarkin birnin Gwari ya yi wa Tinubu nadi a matsayin dakaren birnin Gwari

0
124

Sarkin Birnin Gwari a Jihar Kaduna, Malam Zubair Jibril Maigwari II, ya nada dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Bola Ahmed Tinubu a matsayin “Dakaren Birnin Gwari”.

Tinubu da mukarrabansa sun ziyarci garin Birnin Gwari ne a daren ranar Litinin din da ta gabata domin su kada kuri’u a zaben shugaban kasa da ke tafe.

A yayin ziyarar, Sarkin ya ba wa Tinubu lakabin gargajiya na ‘Dakaren Birnin Gwari’.

Taken yana nufin “babban jarumi na masarauta.”

An nada wa Gwamna Nasir El-Rufa’i na Kaduna rawani a matsayin Sadaukin Birnin-Gwari.