Zan raba tallafin karatun digiri a jami’ar NOUN ga ɗalibai 220 kafin zaɓe – Sha’aban Sharada

0
140

Ɗan takarar gwamna a jihar Kano, ƙarƙashin jam’iyyar ADP, Sha’aban Sharada ya yi alkawarin ɗaukar nauyin karatun digiri na dalibai, ƴan asalin jihar a jami’ar karatu da ga gida, wato National Open University (NOUN).

Sharada, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kano Municipal, ya yi wannan alkawari ne a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a.

Saharada ya yi alƙawarin ɗaukar nauyin ɗalibai 5 daga ko wacce Ƙaramar Hukuma, a cikin ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano, inda adadinsu ya kai 220 kenan.

Ya kuma yi alƙawarin aiwatar da wannan aiki kafin zaɓen 2023.

“Kafin zabe, Zan Dauki Nauyin Karatun Dalibai biyar (5) a kowacce Karamar Hukuma (44) na Jahar Kano har su Gama Degree na farko a National Open University…5×44 = 220 Students,” in ji Sharada.