Kasar Sin ta inganta matakan yaki da COVID-19 a bangaren sufuri

0
100

Kasar Sin ta aiwatar da sauye-sauyen dokoki, a kokarin inganta matakan kandagarki da dakile annobar COVID-19 a fannin sufurin kasar.

Wata takarda da majalisar gudanarwar kasar ta fitar jiya, ta bayyana cewa, kasar za ta yi watsi da ka’idojin da ake amfani da su a motocin dakon kaya, sannan bai kamata kananan hukumomi su aiwatar da matakan da ya wuce kima, don takaita zirga-zirgar irin wadannan motoci ba.

Bugu da kari, za a sanya ma’aikatan sufuri da na jigilar kaya a cikin “jerin muhimman sassa da aka saukaka matakan kandagarki da hana yaduwar COVID-19” a wurin. Sanarwar, ta kuma yi kira da a yi kokarin inganta rayuwar direbobin manyan motoci, da masu jigilar kaya, da ma’aikatan jiragen ruwa.

Ma’aikatar sufuri ta kasar Sin ta ce, a kwanan nan, ta sake yin kwaskwarima kan ka’idoji da yawa don inganta yaki da annobar COVID-19 game da jigilar kayayyaki, da fasinja, jiragen ruwa na cikin gida da sauran sassa.

Kasar Sin ta sanar da wani sabon tsarin daukar matakai, don takaita yaduwar cutar, daga ba da shawarar killacewa a gida ga masu kamuwa da wadanda ba su nuna alamun kamuwa da cutar, zuwa rage gwaje-gwajen cutar, don saukakawa jama’a yin balaguro da shiga wuraren taruwar jama’a.

An bullo da matakan ne dangane da sabon yanayin da ake ciki game da annobar, da yadda kwayar cutar ke sauyawa don shawo kan cutar ta hanyar kimiyya da kuma manufa mafi dacewa.