Ina son Argentina ta lashe kofin duniya a Qatar saboda Messi’ – Ibrahimovic

0
106

Zlatan Ibrahimovic ya bayyana cewa, in da so samu ne tawagar Argentina ta lashe gasar cin kofin duniya dake gudana yanzu haka a Qatar saboda cikar burin tsohon abokin taka ledar sa Lionel Messi.

Ibrahimovic da Lionel Messi sun yi wasa tare tsawon kakar wasa daya a Barcelona, a tsakanin shekarun 2009 da 2010, amma sun ci gaba da kusanci da juna tun bayan da dan kasar Sweden din ya bar Camp Nou ya koma AC Milan da taka leda.

A wannan Jumma’a  Agentinan Messi za su fafata da Netherlands a wasan daf da na kusa da karshe. inda Argentina ke fatan lashe kofin gasar duniya ta uku, kuma ta farko tun daga 1986, wanda ake ganin gasar karshe ga Messi mai shekaru 35.

A bangare daya Brazil zata fafata da Croatia.