Dan shekara 45 ya yi wa ‘yarsa mai shekara 14 fyade a Kwara

0
106

Wata kotun majistare da ke Ilorin a Jihar Kwara ta tisa keyar wani magidanci mai suna Jimoh Lukman mai shekaru 45 a gidan yari bisa zarginsa da yi wa diyarsa mai shekaru 14 fyade.

Rahoton ‘yansanda na farko, ya bayyana cewa Jimoh ya shafe watanni da dama yana aikata wannan kazamin aimi kafin matarsa ​​Sidikat ta kama shi sannan ta kai kararsa ga ‘yansanda.

“Wanda ake tuhumar (Jimoh), ya kasance yana tsoratar tare da yin barazanar yin maganin ‘yarsa da mahaifiyarta idan suka fallasa laifin ga wani ko kuma ga wani jami’in tsaro,” in ji ‘yansanda.

A yayin da ake gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotun a ranar Alhamis, mai shigar da kara, Sanni Abdullah, ya shaida wa kotun karar da ke kunshe da rahoton ‘yansanda, inda ya bukaci a ci gaba da tsare wanda ake kara, sannan ya bukaci kotun ta amince da bukatar.

Mai shari’a Aminat Shittu wadda ta jagoranci shari’ar ta amince da bukatar mai gabatar da kara tare da bayar da umarnin a tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali.