Karancin man fetur: DSS ta baiwa kamfanin mai na NNPC da ‘yan kasuwar man sa’o’i 48

0
220

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bai wa kamfanin man fetur na kasa (NNPC) Limited da masu sayar da mai wa’adin sa’o’i 48 da su samar da Premium Motor Spirit da aka fi sani da fetur ga ‘yan Najeriya.

Kakakin hukumar ta DSS, Peter Afunanya ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsu da ke Abuja bayan ganawar sirri da masu ruwa da tsaki a harkar man fetur.

Ya bayyana cewa kamfanin na NNPC ya tabbatar a yayin taron cewa yana da isassun kayan da za su yi wa ‘yan Nijeriya hidima a lokacin da kuma bayan kakar Yuletide.

Ya ce hukumar ta DSS za ta fara gudanar da ayyukanta a fadin kasar nan idan har suka kasa bin umarnin.

Afunanya ya kuma koka da kalubalen karancin man fetur, inda ya ce an dauki matakin da zai kawo illa ga tsaron kasar.