HOTUNA: Wani dan Najeriya da ya tafi Saudiyya a kan keke daga Jos ya samu gagarumar tarba

0
139

Wani dan Najeriya, Alhaji Aliyu Obobo wanda ya bar Jos, jihar Filato a watan Fabrairun 2021 zuwa Saudiyya a kan keke ya isa kasar.

Alhaji Aliyu Abdullahi Obobo wanda ya bar Jos a watan Fabrairun 2021 zuwa Saudiyya a kan keke ya isa Saudiyya ‘yan mintoci da suka gabata kuma ya samu kyakkyawar tarba daga mahukuntan Saudiyya. Na yi magana da shi ta hannun Khamis Alhasan wanda aiki ya zaunar da shi a can. Sannan kuma shi matafiyin yana magana cikin koshin lafiya.