Tambuwal ya gabatar da kasafin kudin sa na karshe a Sakkwato

0
94

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya gabatar da Naira biliyan 198, 501, 095, 129. 88 a matsayin kasafin kudin shekarar 2023 a gaban Majalisar Dokokin Jihar.

Kasafin wanda shi ne na karshe da Gwamna Tambuwal ya gabatar a mulkinsa na shekaru takwas a wa’adin zango biyu da ya jagoranta, ya karu da kashi 26.7%, wato Naira biliyan 10 a kan na 2022 wanda ya gabatar a kan Naira biliyan 188, 429, 495, 847. 63.

Kudaden albashi da tafiyar da al’amurran yau da kullum sun samu naira bilyan 41 338, 449, 185. 12 da 42 756 507 973. 65, sai kuma manyan ayyuka da suka samu naira biliyan 111, 406, 137, 971. 11.

Kamar a kowane kasafi, fannin ilimi ya samu kaso mafi yawa na biliyan 36, 991, 319, 548. 53 wato kashi 18.6% sai fannin lafiya da ya zo na biyu da naira biliyan 25, 208, 374, 170. 49, sai fannin aikin gona da ya samu naira biliyan 11, 010, 553, 897. 62 (5.5%) a yayin da samar da ruwan sha ya samu naira biliyan 4, 317 715 705. 45 (2.2%)
Sauran fannoni sun samu naira biliyan 116, 917, 145, 031. 49 wato kashi 58.9%.

Manyan ayyuka sun samu kashi 58. 9% na bakidaya kasafin a yayin da al’amurran yau da kullum suka samu kashi 41. 1%. Tambuwal ya ce kasafin kudin zai ba da damar kammala dimbin ayyukan da aka assasa da muhimman ayyukan da za a rika tunawa wadanda gwamnatinsa ta aiwatar.

Gwamnan ya godewa mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, sarakunan gargajiya, malaman Addini da daukacin al’ummar jihar Sakkwato baki daya kan goyon bayan da suka baiwa Gwamnatin sa.

Tambuwal ya kuma bukaci hadin kan manbobin Majalisar dokokin jihar Sakkwato domin tabbatar da kudurorin Gwamnatin sa ta hanyar aiwatar da ayyukan raya jiha da ci-gaban al’umma.