Qatar 2022: Brazil ta casa Koriya ta kudu

0
105

Kasar Brazil ta casa Koriya ta Kudu a gasar cin kofin duniya da ake yi a Kasar Qatar da ci 4 da 1.

Brazil ta fara wasan nata ne, bayan fitowa daga rukuni, inda ‘yan wasanta daban-daban har guda hudu suka zura mata kwallaye.

‘Yan wasa irin su Vinicius, Neymar, Richarlson da Paqueta ne suka jefa wa Brazil kwallo a raga.

Yanzu haka dai Brazil ta matsa zagaye na gaba, inda za ta kara da Kasae Croatia.

Kasashen irin su Argentina, Ingila, Croatia, Brazil, Faransa da Holland duk sun tsallaka zagaye na gaba.