Mayakan ISWAP da Boko Haram sun tafka kazamin fada a tsakanin su

0
99

Rikicin da ya barke tsakanin bangaren mayakan Boko Haram da ISWAP, wanda aka ce an kashe ‘yan ta’adda da dama a cikin kwanaki ukun da suka gabata.

Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya a yankin tafkin Chadi, ya tattaro cewa fitaccen shugaban kungiyar Boko Haram, Ali Ngulde, a ranar 3 ga watan Disamba, ya jagoranci daruruwan mayaka dauke da muggan makamai daga tsaunin Mandara, inda suka kai farmaki kan sansanin ISWAP a wani gagarumin farmaki da suka kai musu.

Kazalika majiyoyin leken asiri sun shaida wa Makama cewa an fara arangama ne a sansanin Yuwe, wanda ya haifar da kazamin musayar wuta da mayakan Ngulde suka yi galaba a kan mayakan ISWAP tare da kashe 12 daga cikinsu sannan suka kwace makaman su.

Ba da jimawa ba, majiyoyi sun ce mayakan na Boko Haram sun yi gaggawar tattara karin mayakan daga sansanin Abu Ikilima da ke Gaizuwa, Gabchari, Mantari da Mallum Masari.

A cewar kwararre na yaki da ‘yan ta’addan, an kashe mayakan ISWAP sama da 23 a ranar 4 ga watan Disamba, lokacin da bangaren Shekau na kungiyar Boko Haram suka rabu gida biyu, suka kai farmaki kan ISWAP a Ukuba, Arra da Sabil Huda.

Zagazola ya kara da cewa, a daren Lahadi, an ga wata tawagar mayakan da ke sansanin ISWAP a kusa da Kawuri da Aulari, inda a safiyar ranar Litinin wani babban shugaban ISWAP, Ba’ana Chingori, ya jagoranci wata tawagar mayakan da suka kai farmaki kan mayakan Boko Haram.

Rikicin da ya barke tsakanin bangarorin ‘yan ta’addar ya yi sanadiyar mutuwar mayaka da dama.