Dan takarar jam’iyyar Labour Party ya rasu a Imo

0
143

Dan takarar majalisar wakilai na jam’iyyar Labour a Okigwe, jihar Imo, Mista Irouno Chukwunonye ya rasu.

Iruono ya fadi da yammacin ranar Litinin kuma an tabbatar da mutuwarsa da sanyin safiyar Talata.

Marigayin dan siyasan wanda kuma mamba ne a majalisar yakin neman zaben kujerar shugaban kasa  na Peter Obi, ya rasu a Owerri a yau, Talata.

Ya kasance Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Imo akan nishadi,ya kuma kasance shugaban Hukumar Nishaɗi da Carnival ta Jihar Imo.