An yanke wa dan kungiyar asiri hukuncin kisa a jihar Ekiti

0
100

Wata babbar kotun Jihar Ekiti da ke zamanta a Ado Ekiti, ta yanke wa wani Segun Iwaetan hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin zama dan kungiyar asiri da kuma laifin yi wa budurwa ‘yar shekara 20 fyade.

Kotun ta yanke wa matashin mai shekaru 24 hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin yi wa makwabciyarsa fyade, waadda dalibar Kwalejin Fasaha ta Ado Ekiti ce.

An gurfanar da Iwaetan akan tuhume-tuhume bakwai da suka shafi fyade, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, da shiga kungiyar asiri, da sauran laifuka.

A cewar tuhumar, “Segun Iwaetan da Atila Iwaetan (a halin yanzu) a ranar 16 ga Janairu, 2021, sun hada baki wajen yin sata, sun shiga shagon wani Olayemi Oyerinde, sun karbi kadarori irin su rigar polo 15, wando jean 50, silifas na fata guda 30 da dai sauransu, wanda ya kai sama da Naira miliyan 1.8.

“A ranar 5 ga watan Fabrairu, 2021, Iwaetan ya yi wa wata daliba ‘yar shekara 20 fyade a Titin Odo Ado, Ado Ekiti, yayin da ya mallaki bindigogi biyu ba bisa ka’ida ba. An same shi, a ranar 10 ga watan Fabrairu, 2021 da kasancewa memba na kungiyar asiri ta ”

‘Eiye confraternity’,” in ji shi.

Wadda aka yi wa fyaden a cikin shaidar ta, ta bayyana cewa, “A ranar, wadda ake kara ya samu shiga dakina da misalin karfe 3 na dare, kuma ya nuna min bindiga yayin da ya umarce ni da kada in yi ihu idan ba haka ba ya harbe ni.

“Ya umarce ni da in cire kayana kuma ya yi lalata da ni ta karfin tsiya.

“a lokacin da ya yi min fyade, har yanzu ni budurwa ce. Bayan haka, ya roke ni gafara kuma ya ce kada in gaya wa kowa game da lamarin.”

Lauyan mai gabatar da kara, Albert Adeyemi, ya kira shaidu biyar sannan ya gabatar da bayanin wanda ake kara, sammacin bincike, bindigogi biyu na gida a matsayin shaida da kuma rahoton likita.

Mai shari’a Adeniyi Familoni, wanda ke yanke hukuncin, ya yanke wa wanda ake kara hukunci a kan tuhume-tuhume hudu.

Alkalin ya ce, “An yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin kamar haka: hada baki da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, an yanke masa hukuncin daurin shekaru 12 a gidan yari kowane ba tare da wani zabin biyan tara ba, za a ci gaba da zartar da hukunci a lokaci guda daga ranar da aka kama shi da kuma tsare wanda ake tuhuma.

“Akan fyade, kotu ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga wanda ake kara,” yayin da saboda kasancewa memba na kungiyar asiri ta Eiye confraternity, alkali ya shaida wa wanda ake kara cewa, “Hukuncin da wannan kotu ta yanke a kan ku shi ne a rataye shi har sai kun mutu.