An kashe mutum 8, an kone gidaje 47 a rikicin manoma da makiyaya a Borno

0
112

Kwasihinan ’Yan Sandan jihar Borno, Abdu Umar ya ce mutum 47 ne aka hallaka, aka kuma kone gidaje  takwas a wani fada tsakanin makiyaya da manoma a jihar.

Kwamishinan ya sanar da hakan ne a yayin wani taro da shugabannin kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti-Allah (MACBAN) tare da manoma a hedikwatar a rundunar da ke Maiduguri.

Ya ce rahoton da suka samu ya nuna cewa rikicin da ya barke ne a Karamar Hukumar Bayo, a inda mutane takwas ne aka kashe, cikinsu har da yara kanana uku.

Abdu Umar ya kuma ce tashin hankalin ya dami jami’an tsaro, la’akari da yadda suke bakin kokarinsu na dawo da zaman lafiya a yankin.

Ya kuma ce, ’yan sanda sun samu nasarar cafke wasu da ake zargi na da hannu a aikata laifin, kuma za a gurfanar da su gaban kuliya bayan kammala bincike.