Ku zabi ’yan takarar PDP amma banda na Shugaban Kasa – Wike

0
119

Gwamna Nyesom Wike ya bukaci al’ummar Jihar Ribas da su zabi jam’iyyar PDP a kowane mataki amma ban da kujerar Shugaban Kasa a babban zabe mai zuwa.

Wike ya kuma bukaci al’ummar jihar da su ba shi lokaci har ya kai ga bayyana musu mutumin da za su zaba a kujerar shugaban kasa.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a lokacin kaddamar da wani aikin titi a yankin Rukpoku-Rumuapu-Izo-Ogbodo-Ogwuruta a Karamar Hukumar Obio/Akpor ta jihar.

“Ku tabbatar kun zabi jam’iyyar da za ta yi muku aiki.

“Kun san wadanda za ku zaba – ku zabi dan takararmu na gwamna, ku zabi ‘yan takararmu na majalisar wakilai, ku zabi ‘yan takararmu na Sanata, ku zabi ‘yan takararmu na majalisa.

“Duk wadanda muka ambata, ku tabbatar kun zabe su. Shi kuwa dayan [dan takarar shugaban kasa], nan ba da jimawa ba za mu hadu a gidajenmu, don yanke shawarar wanda za mu zaba.”

Bayanai sun ce Wike da wasu gwamnoni hudu na jam’iyyar PDP da ake kira G5 sun shiga takun-saka da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar da kuma shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu.