Gwamnatin Kano ta janye dokar takaita zirga-zirgar adaidata sahu a jihar

0
128

Gwamnatin Kano ta sanar da janye dokar da ta haramta wa ’yan babura masu kafa uku da aka fi sani da Adaidaita Sahu zirga-zirga a wasu manyan titunan jihar.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar (KAROTA) ta fitar a Yammacin wannan Larabar.

Da yake zantawa da manema labarai a birnin na Dabo, Shugaban KAROTA, Baffa Babba, ya ce sun yanke wannan shawara ce sakamakon la’akari da rashin kammala shirye-shirye daga bangaren kamfanin motocin da zai rika jigilar fasinjoji a manyan titunan.

A cewar Baffa Babba, akwai tsaiko da aka samu na soma ayyukan sufurin daga ranar Laraba, 30 ga watan Nuwamba, a sakamakon rashin isassun motocin bas-bas da za su rika zirga-zirga a kan manyan titunan.

Da wannan uzuri ne Shugaban KAROTAr yake cewa an jingine sabuwar dokar har sai abin da hali ya yi.

A ranar Talata ce gwamnatin Jihar Kano ta bakin Hukumar KAROTA ta sanar da hana baburan masu kafa uku bin wasu tituna a birnin, inda ta maye gurbinsu da dogayen motocin safa-safa da ta kawo.