Gwamnatin jihar Kano ta haramta wa Yan Adaidaita Sahu bin manyan Titunan jihar Kano

0
106

Gwamnatin jihar Kano ta hannun Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta haramta wa matuƙa Baburin Adaidaita Sahu min manyan titunan jihar nan daga gobe Laraba 30 ga watan Nuwamba, 2022.

Gwamnatin ta ɗauki matakin ne bayan da ta samar da manyan motocin da za su dinga ɗaukar al’umma a titinan da aka haramtawa yan Adaidaita Sahun

Sanarwar ta bayyana cewa an haramta wa Direbobin Baburin Adaidaita Sahun bin titinan Amadu Bello By Munduɓawa zuwa Gazawa da titin Tal’udu zuwa Gwarzo

Gwamnatin ta bayyana cewa ta tanadi manyan motocin sufuri domin sauƙaƙawa al’umma bin waɗannan hanyoyi

Gwamnatin ta ƙara da cewa za ta sanar da ranar da matuƙa Adaidaita Sahun za su daina bin wasu manyan titinan da zarar gwamnatin ta samar da Ababen hawan da al’umma za su yi amfani da su a waɗannan hanyoyi.