‘Yan sanda sun cafke mutane 2 dauke da katin zabe 468

0
115

Rundunar ‘yan sanda ta kama wasu mutane biyu da ke rike da katin zabe na dindindin PVC har guda 468 a wurinsu.

Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye, a ranar Lahadi.

A cewar sanarwar, wadanda suka aikata laifin; Nasiru Idris, an same shi da PVC guda 101 a jihar Sokoto, wani kuma (ba a ambaci sunansa ba) an kama shi da PVC guda 367 a jihar Kano.

Okoye ya bayyana cewa laifin nasu ya sabawa sashe na 117 da 145 na dokar zabe ta 2022.

Sanarwar ta kara da cewa a halin yanzu wadanda suka aikata laifin suna amsar hukuncin da ya dace.