2023: Kotu ta tabbatar wa Machina takarar sanatan Yobe ta Arewa

0
102

Kotun Daukaka Kara ta sake tabbatar da Bashir Machina a matsayin dan takarar Sanatan Yobe ta Arewa na jam’iyyar APC.

A wani hukunci da kwamitin mutum uku karkashin jagorancin shugabar kotun, mai shari’a Monica Dongban-Mensen ta yanke, ta yi watsi da karar da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ya shigar yana kalubalantar cancantar Machina.

Lawan, ya shigar da kara ne yana kalubalantar hukuncin da mai shari’a Fadimatu Aminu, ta babbar Kotun Tarayya da ke Damaturu ta zartar na tabbatar da Machina a matsayin dan takara.

A ranar 28 ga watan Satumba, 2022, Fadimatu ta ayyana Machina a matsayin wanda ya lashe zaben fid-da-gwanin da jam’iyyar APC ta gudanar a watan Mayun 2022.

Wannan dai ta faru ne yayin da kotun ta tabbatar da cewa Sanata Ahmed Lawan ya nemi takarar Shugaban Kasa a zaben fid-da-gwanin da jam’iyyar APC ta gudanar a watan Yuni, saboda haka ba shi da hurumin neman tikitin kujerar Sanatan Yobe ta Arewa.

Sakamakon haka, alkalin kotun ta umarci APC da ta mika sunan Machina ga Hukumar Zabe ta Kasa INEC a matsayin wanda ya yi nasara a zaben fid-da-gwanin da aka gudanar a watan Mayun.

Aminiya ta ruwaito cewa, Sanata Lawan na daya daga cikin wadanda suka sayi fom din neman takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC kuma ya shiga zaben fid-da-gwanin wanda Bola Ahmed Tinubu ya lashe.

Bayanai sun ce Machina dai ya nemi takara a jam’iyyar APC kuma ya yi nasara a yunkurinsa na maye gurbin kujerar Sanatan Yobe ta Arewa a zaben badi.

Sai dai an nemi Machina da ya sauka da ya janye, amma ya dage cewa ba zai janye wa Shugaban Majalisar Dattawan ba.

Bayan da aka soma rudani kan wanda zai tsaya takarar ce kwatsam sai jam’iyyar APC ta mika wa INEC sunan shugaban Majalisar Dattawan a matsayin dan takararta na Sanatan Yobe ta Arewa.

Sai dai Machina a karar da ya shigar, ya roki kotun da ta bayyana shi a matsayin halastacce kuma zababben dan takarar sanatan Yobe ta Arewa na jam’iyyar APC a Zaben 2023.