Dan shekara 12 ya yi garkuwa da yarinya mai shekara 3 a Bauchi

0
148

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Bauchi, ta kama wani yaro mai shekara 12 da ake zargi da yin garkuwa da wata yarinya mai shekara uku a duniya.

Yaron dai ya yi garkuwa da yarinyar ne a wani filin kwallo da ke garin Magama Gumau, sannan ya kira mahaifinta ya bukaci a biya shi Naira dubu 150.

Kakakin rundunar a Jihar, SP Ahmed Wakil ne ya tabbatar da kamun a cikin wata sanarwa a Bauchi ranar Asabar.

A cewarsa, “Bayanan da rundunarmu ta samu sun nuna cewa ranar 23 ga watan Nuwamban 2022, wajen misalin karfe 5:40 na yamma, wani mutum mai shekara 56 da ke da shago a Magamar Gumau, ya sami kiran waya daga wani yaro, yana bukatar a ba shi Naira dubu 150 a matsayin fansar ’yarsa da aka sace.

“Binciken farko-farko ya nuna mana cewa wanda ake zargin ya yaudari yarinyar ne zuwa wani waje da ke kusa da wani filin kwallo, sannan ya kira mahaifinta ya nemi kudaden.

“Da jin haka, mutumin ya katse wayar, shi kuma yaron ya ci gaba da kira. Bayan wani lokaci sai mahaifin yarinyar ya sake kiran wayar, inda ya gane muryar yaron, saboda dama ya san shi.

“Da yaron ya ji alamun an gane shi, sai ya yi maza ya kashe wayar. Daga nan kuma sai ya yi sauri ya mayar da ita gidansu, inda ya ce musu wai ya ganta ne a kusa da filin kwallo tana kuka.

“Ganin haka ne ya sa iyayen yarinyar suka kai rahoton batun ga ’yan sanda. Bayan an titsiye shi kuma, sai ya ce daga Kano ya zo Bauchi neman kudi tare da ’yan uwansa, inda ya tara kudi ya sayi waya,” inji Kakakin.

Ya kuma ce bincikensu ya gano cewa yarin ya koyi garkuwar ce lokacin da a baya aka taba sace abokinsa a Kano, sai da aka biya kudin fansa kafin a sake shi.

Wakil ya kuma ce za su tisa keyar yaron zuwa gaban kuliya da zarar sun kammala bincike.

Kakakin ya kuma shawarci iyaye da su rika sa ido sosai kan kaiwa da komowar ’ya’yansu domin kaucewa fadawa hannun miyagu.

AMINIYA