Ba zan taba janye wa kowa ba – Kwankwaso

0
114

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa ba zai taba janye wa wani dan takara ba a zaben shugaban kasa a 2023.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a ganawarsa da tawagar Editoci da wakilan kafafan yada labarai da ya gudana a Ikeja da ke Jihar Legas.

“Dole mu zauna wajen tattauna yadda za mu iya raba kasar nan da basuka. Yana da matukar muhimmanci mu dauki matakan yadda za mu magance matsalolin bashi,” in ji shi.

A hannu guda kuma, jigon NNPP ya bukaci gudummuwar dukkanin masu ruwa da tsaki da ke kasar nan a kan matsaloli tun daga kan ilimi, noma, man da iskar gas da kuma matsalar tsaro, inda ya tabbatar da cewa za a samu gagarumar ci gaba a fannin mai da iskar gas matukar aka kula da kamfanin mai na kasa (NNPC) yadda ya kamata domin amfanar da kowa.

Ya ce bisa kwarewarsa a matsayinsa na tsohon gwamnan Jihar Kano, ya sha mamban da sauran ‘yan takara da ke neman shugabancin Nijeriya. Kwankwaso ya kara da cewa ya san yadda zai kula da dukiyar al’umma wanda shi ne ya bambanta shi da sauran ‘yan takarar shugaban kasa.

“A yanzu haka mun ji dadin kasancewa akwai dokar da za ta tabbatar da bunkasa kamfanin NNPC, sannan a shirye muke mu janyo masu zuba jari a kasar nan.

“Za mu ci gaba da goyon bayan dokar domin tabbatar da cewa fannin man da iskar gas ya amfanar da kowa,” in ji shi.